Kungiyar haɗakar kungiyoyin Fulani na jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ta na jiha, Ahmad Chanji Mangari, ta kai ziyara a Karaye domin sauraron koke-koken makiyaya a yankin.
Kungiyar ta gana da Turakin Karaye, Alhaji Abdullahi Aminu, wanda kuma shi ne Hakimin Karaye, domin neman tabaraki da kuma sanar da shi matsalolin da suka shafi makiyaya. Cikin koke-koken da aka gabatar cinye filayen kiwo don noma da wasu dalilai na daban, katse hanyoyin wucewar dabbobi da kuma amfani da wuraren shan ruwa na shanu wajen noma da dai sauran su.
Makiyaya a yankin sun kuma roƙi gwamnati ta gina makarantun firamare ga yara ‘ya’yan makiyaya a wurare da dama, ciki har da Kumbugawa, Badomawa, Tsauni Gidan Alhaji Hamza, Turawa Mauri da Madobawa. Haka nan sun bukaci a gina makarantu a Yawuriji da Magajin Hajjin Kwanar Bauni.
Baya haka, shugabannin kungiyar sun kai ziyara ofishin ‘yan sanda na Karaye, inda suka gana da DCO Auwalu Yahaya da kuma Sufeto Abubakar Hussaini mai kula da bangaren laifuka.

Wadanda suka raka mataimakin shugaban kungiyar a ziyarar sun haɗa da mai binciken kudi na ƙungiyar, Lamido Idris, da kuma jami’in hulɗa da jama’a ɗin ƙungiyar, Idris Shuaibu Bayero.